Sudan Ta Kudu : Riek Mashar Ya Isa Birnin Juba
Oct 31, 2018 12:03 UTC
Jagoran 'yan tawaye a Sudan ta Kudu, Riek Mashar, ya isa Juba babban birnin kasar, inda zai halarci bikin yarjejeniyar zaman lafiya da aka cimma da gwamnati a watannin baya.
Hakan dai zai baiwa Mista Machar komawa kan tsohon mukaminsa na mataimakin shugaban kasar Salva Kiir, kamar yadda yarjejeniyar ta tanada.
Marabin jagoran 'yan tawayen na Sudan ta Kudu ya sanya kafa a fadar mulkin kasar tun watan Yuli na 2016, bayan da ya tsere sakamakon barkewar rikici tsakanin mayakan dake masa biyaya da kuma dakarun gwamnatin kasar.
Tags