An Gano Gawar Janar Alkali
Sojojin Najeriya Sun Sanar Da Gano Gawar Janar Idris Alkali
An ganogawar ne dai a cikin wata tsohuwar rijiya da ke yankin Guchwet a karamar hukumar jos ta kudu kamar yadda Birgediya janar Umar Muhammad ya sanar.
Alkaki ya rike mukamin babban jami'in tafiyar da sha'anin mulki a babbar shalkwatar sojan Najeriya da ke Abuja. An sanar da bacewarsa ne a ranar 3 ga watan Satumba bayan da ya bar Abuja zuwa Bauchi.
Babban hafsan hafsoshin sojan Najeriya Laftanar Janar Tukur Buratai ya kafa kwamiti domin binciko janar din da ya bace.
Birgadiya janar Umar Muhammad wanda shi ne kwamandan rundunar sojojin Najeriya ta 3 ya ce wani daga cikin wadanda ake zargi da hannu a bacewar tsohon janar din ne, ya kai su inda rijiyar da aka jefa gawar take.
Umar Muhammad ya kara da cewa bayan da su ka gano gawar janar din, yanzu abin da ya saura shi ne su tabbatar da cewa wadanda ake zargi da hannu a cikin bacewar janar an kamo su sun kuma fuskanci shari'a.