Najeriya: An Sace Kansiloli Biyu A Jahar Katsina
Oct 31, 2018 18:02 UTC
Kansilolin biyu da aka sace sun fito ne daga karamar hukumar Safana da ke jahar katsina a arewacin kasar Najeriya.
Jaridar Daily Trust da ta dauki labarin ta ce; Mutanen da aka yi garkuwa da su su ne; Hussain Wanzam wanda kansila ne akan harkokin kudi, da kuma Bishir Dan Jokko mai kula da tsafta da kuma ruwa a karamar hukumar ta Safana.
An kame su ne akan hanyarsu ta zuwa garin Batsari bayan tashin su daga aiki.
Har zuwa yanzu dai masu garkuwar da su ba su ambaci abin da suke son a ba su ba kafin su sake su.
Yin garkuwa da mutane domin karbar fansar kudade ya fara zama ruwan dare a arewacin Najeriya.
Tags