MDD Ta Nuna Damuwa Akan Karuwar Ayyukan Ta'addanci A Libya
Manzon musamman na MDD a kasar Libya Ghassan Salamah ne ya bayyana damuwarsa akan yadda wasu sassa na kasar da su ka hada da birnin Tripoli su ka zama sansanonin 'yan ta'adda
Ghassan Salamh wanda yake ziyarar aiki a kasar Moroko ya jaddada wajabci kawo karshen rikice-rikicen da kasar take fama da su, da komawa kan teburin tattaunawa domin warware sabani a siyasance.
Ofishin da yake wakilatar Majalsiar Dinkin Duniya a kasar ta Libya ya fitar da wani bayani wanda a cikin ya kunshi yin tir da harin ta'addancin da kungiyar Da'esh ta kai a garin al-fuqaha da ke tsakiyar kasar ta Libya a ranar Lahadin da ta gabata.
Ayyukan ta'addancin suna karuwa a cikin kasar ta Libya wacce ta ke karatar lokacin gudanar da zabukan shugaban kasa da na 'yan majalisar dokoki a cikin watan Disamba na wannan shekara.