Amnesty Int. Ta Yi Allawadai Da Kisan 'Yan Shi'a A Najeriya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i33868-amnesty_int._ta_yi_allawadai_da_kisan_'yan_shi'a_a_najeriya
Kungiyar kare hakkin bil adama ta Amnesty Int. ta yi Allawadai da kakkausar murya kan kisan da sojoji da 'yan sandan Najeriya suka yi wa mabiya mazhabar shi'a a karkashin harkar musulunci a Abuja.
(last modified 2019-08-10T14:54:46+00:00 )
Nov 01, 2018 05:11 UTC
  • Amnesty Int. Ta Yi Allawadai Da Kisan 'Yan Shi'a  A Najeriya

Kungiyar kare hakkin bil adama ta Amnesty Int. ta yi Allawadai da kakkausar murya kan kisan da sojoji da 'yan sandan Najeriya suka yi wa mabiya mazhabar shi'a a karkashin harkar musulunci a Abuja.

Daraktan kungiyar Amnesty Int. a Najeiya Osai Ojigho ta fadi jiya cewa, suna da kwararan dalilai da suke tabbatar da cewa jami'an tsaron gwamnatin Najeriya sun yi amfani da karfin da ya wuce doka ta hanyar yin amfani da harsasai masu rai wajen kisan mabiya mazhabar shi'a da suke gudanar da jerin gwano na lumana.

Ta ce wannan ba abu ne da za a lamunta da shi ba, domin kuwa jerin gwano ne na lumana da fararen hula suke gudanarwa wadanda ba su dauke da makamai, a kan haka babu wani dalili da jami'an tsaron suke da shi na yin amfani da bindiga domin kashe 'yan kasa saboda jerin gwano, wannan ya sabawa dukkanin dokoki na duniya.

Bayanin na Amnesty ya tabbatar da cewa akwai mutane kimanin arba'in wadanda ake da tabbacin cewa sun rasa rayukansu, duk kuwa da cewa wasu bayanan sun ce mutane 45, yayin da wasu kimanin  122 kuma sun samu raunuka sakamakon harbin su da bindiga.

Kungiyar ta kirayi gwamnatin da ta gaggauta gudanar da bincike kan wannan lamari, domin hukunta jami'an tsaron da suka aikata wannan aiki.