Riek Machar Ya Koma Gida
Bayan kwashe lokaci mai tsaho yana hijra a kasashen waje, tsohon shugaban kasa kuma madugun 'yan tawayen kasar Sudan ta kudu ya koma birnin Juba.
Rahotani dake fitowa daga kasar sudan ta kudu sun tabbatar da cewa a jiya laraba madugun 'yan tawayen kasar Riek Machar ya isa birnin Juba, inda ya samu kyakkyawar tarbe daga mahukuntan kasar gami da magoya bayansa, an gudanar da bikin birnin yarjejjeniyar zaman lafiya tsakanin bangarorin biyu da suka kwashe sama da shekaru uku suna fada da juna.
Mr. Machar wanda ya bar kasar sama da shekaru biyu da suka gabata, ya koma ne bisa sharadin kama aikinsa na mataimakin shugaban kasa, kamar yadda yarjejeniyar da aka cima a watan jiya ta nunar.
A baya dai an sha irin wannan yarjejeniya ba tare da nasara ba, a wani yunkuri na dawo da zaman lafiya a Sudan ta Kudun da yakin basasa ya kassara rayuwar akalla mutum miliyan hudu.