Bukatar Amurka Na Binciken Rikicin Sojoji Da 'Yan Shi'a A Najeriya
Binciken da Amurka ta bukata ya biyo bayan da kungiyar ta Islamic Movement in Nigeria, ta ce an kashe mabiyanta fiye da 50 sakamakon rikicin baya baya nan a wasu yankunan Abuja.
Sanarwar da ofishin jakadancin Amurka a Najeriya ya fitar, ta nemi gwamnatin Najeriya ta gudanar da cikakken bincike kan rikicin, wanda ta ce lamarin kashe kashen 'yan shi'an na da matukar damuwa.
Amurkar ta kuma nemi gwamnatin ta Najeriya, data dau duk matakan da suka dace domin neman bayyani daga wadanda suka sabawa dokar Najeriyar, tare kuma da bukatar dukkan bangarorin su kai zuciya nesa.
A halin yanzu dai ana ta samun sabani akan alkalumman mutanen da rikicin ya rusa dasu, inda ita kungiyar 'yan shi'an ta IMN karkashin jagorancin Sheikh Ibrahim Zakzaky ke cewa an kashe mata mambobi fiye da 50, ita kuwa rundinar sojin Najeriya da 'yan sanda kasar musanta hakan sukayi suna masu cewa mutum shida ne suka mutu a rikicin.
Saidai a nata bangare kungiyar kare hakkin bil adama ta kasa da kasa, Amnesty International, ta ce mutum 45 suka mutu a rikicin na baya bayan nan, shida a ranar Asabar data gabata, sai kuma 39 a ranar Litini, ranar da kuma mutum 122 suka jikatta.
Kungiyar ta Amnesty ta kuma ce tana da kwararen hujojji dake nuna yadda sojoji da 'yan sandan na Najeriya sukayi amfani da bindigogi masu sarrafa kansu kan almajiran na Malam Ibrahim Zakzaky dake zanga-zangar lumana a birnin Abuja da gewayensa.
A tsakanin ranakun Asabar zuwa Talata ne dai rikicin ya barke tsakanin 'yan kungiyar ta IMN dake tattakin arba'in na zagayowar kisan jikan mazon Allah Iman Hussain (AS), da kuma bukatar neman a saki jagoran nasu Ibrahim Zakzaky, da gwamnatin kasar ke tsare da shi yau kusa da shekara uku.
Ana dai tsare da jagoran harkar ta Islamiya IMN, wato Mal. Ibrahim Zakzaky, da mai dakinsa, tun bayan mummunan rikicin Zaria dake jihar Kaduna a arewacin kasar a watan Disamba na 2015.
Kuma tun lokacin kungiyoyin kare hakkin bil adama ke zargin sojojin na Najeriya da kashe 'yan shi'a sama da 300, tare da binne su a cikin wani makeken kabari, saidai rundinar sojin Najeriyar na ci gaba da musanta hakan.
Tun dai bayan rikicin na 2015, sau biyu kawai jagoran kungiyar ta harkar Islamiya IMN ya bayyana a bainar jama'a.
A karshen shekara 2016 dai wata babbar kotun Abuja ta bada umurnin sakin jagoran kungiyar wanda ta ce ana tsare da shi ba bisa ka'ida ba, amma har yanzu gwamnatin Najeriyar bata aiwatar da wannan umurnin kotun ba.