MDD Ta Yi Allawadai Da Kisan Mutane A Harin Boko Haram
Majalisar dinkin duniya ta yi allawadai da harin da mayakan boko haram suka kai kan sansanin yan gudun hijira a birnin Maiduguri na jihar Borno a tarayyar Najeriya.
Jaridar Premiumtimes ta Najeriya ta nakalto jami'i mai kula da ofishin majalisar a Abuja Edward Kallon yana cewa harin ya auku ne a daren laraba da ya gabata, sannan wannan shi ne hari mafi muni a baya bayan nan, wanda mayakan boko haram suka kai kan fararen hula.
Labarin ya kara da cewa hare-haren sun yi sanadiyyar mutuwar mutane 8 da kuma kama wasu mata. Majalisar ta kara da cewa yan gudun hijira kimani 12,600 ne suke samun mafaka a sansanin tun bayan kauracewar yankunansu da suka yi a shekarun bayan, sanadiyyar hare-haren mayakan na boko haram.
Jami'i mai kula da bangaren sadarwa na hukumar OCHA, ita ma ta majalisar dinkin duniya ta bayyana cewa an kai harin ne a sansanin yan gudun hijira da ke kusa da kauyen Dalori kusa da birnin Maiduguri a dai-dai lokacin faduwar rana, don haka mayakan na boko haram sun sace kayakin abicni a cikin gidajen mutane da dama a kauyen.