Najeriya: An Gurfanar Da Yan Shi'a 130 A Gaban Kotu
A jiya Alhamis ne 'yansanda a Abuja na tarayyar Najeriya suka gurfanar da yan shi'a na "Islamic Movement In Nigeria" IMN su 130 a gaban wasu kotuna a yankin Wuse 2.
Jaridar Punch ta Najeriya ta kara da cewa an gurfanar da mutanen 130 ne a gaban alkalai 4 a kotuna daban daban a wuse 2, kuma 12 daga cikinsu mata ne, wasu ma sauna shayarwa.
Laifuffukan da ake tuhumarsu da su dai, sun hada da taron da babu izini, da kuma tada hankali a cikin gari. Alkalai a kotuna masu lamba 11,15,17 sun bada belin wadanda aka gurfanar da su a gabansu, wato mutane 90 tare da kudade wadanda suka kama daga naira dubu 50 zuwa dubu 500. Har'ila yau tare da masu tsayawa ko wannensu.
Bayan haka dai 'yansandan sun maida dukkan mutane 130 zuwa gidan kaso kafin wadanda suka sami beli su cika sharuddan sakinsu.
Dukkanin wadanda ake tuhuman dai sun musanta laifuffuka da ake tuhumarsu da su..