An Hallaka 'Yan Ta'adda 19 A Kasar Masar
(last modified Sun, 04 Nov 2018 19:20:53 GMT )
Nov 04, 2018 19:20 UTC
  • An Hallaka 'Yan Ta'adda 19 A Kasar Masar

Jami'an tsaron Masar sun sanar da hallaka wasu 'yan ta'adda 19 daga cikin wadanda suka kaiwa motar Kibdawa hari.

Tashar talabijin din Almayadeen dake watsa shirye-shiryenta daga kasar Labnon ta nakalto ma'aikatar cikin gidan Masar jami'an tsaron kasar sun samu nasarar hallaka 'yan ta'adda 19 wadanda suka kaiwa motar 'yan kabilar Kibdawa hari a yankin Sohag.

A ranar juma'ar da ta gabata ce wadanda 'yan ta'adda suka kaiwa wata Bas dake dauke da 'yan kabilar Kibdawa a jahar Sohag dake kasar ta Masar, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutum 9 tare da jikkata wasu 14 na daban.

Jim kadan bayan kai harin, kungiyar ta'addancin nan ta Da'esh ta dauki alhakin kai harin.