Akalla Mutane 4 Sun rasa Rayukansu A Wani Harin Bam A Somalia
(last modified Mon, 05 Nov 2018 06:19:27 GMT )
Nov 05, 2018 06:19 UTC
  • Akalla Mutane 4 Sun rasa Rayukansu A Wani Harin Bam A Somalia

Mutane 4 ne aka tabbatar da cewa sun rasa rayukansu sakamakon wani harin bam da aka kai a birnin Magadishou na kasar Somalia.

Kamfanin dillancin labaran Xin Huwa ya bayar da rahoton cewa, an tayar da bam din ne a lokacin da wata motar jami'an sojin kasar ta Somalia suke sintiri a wata unguwa da ke cikin birnin Magadishou, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar sojoji uku a nan take da kuma wani farar hula guda.

Babu wani mutum ko wata kungiyar da suka dauki alhakin harin, amma tuni mahukuntan kasar ta Somalia suka dora alhakin hakan a kan kungiyar alshabab mai dauke da akidar wahabiyanci da ke alaka da kungiyar alka'ida wadda ke da'awar jihadi.

A lokuta da dama dai kungiyar ta Alshabab ta kai irin wadannan hare-hare da ma wadanda suka fi hakan muni a cikin birnin magadishou, da ma wasu biranan kasar ta Somalia, lamarin da kawo yanzu ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama.