Najeriya : Kungiyar ASUU Ta Tsunduma Yajin Aiki
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i33946-najeriya_kungiyar_asuu_ta_tsunduma_yajin_aiki
Kungiyar malaman jami'a ta Najeriya, cewa da ASUU ta shiga wani yajin aikin sai baba-ta-gani daga yau Litini.
(last modified 2018-11-05T11:14:59+00:00 )
Nov 05, 2018 11:14 UTC
  • Najeriya : Kungiyar ASUU Ta Tsunduma Yajin Aiki

Kungiyar malaman jami'a ta Najeriya, cewa da ASUU ta shiga wani yajin aikin sai baba-ta-gani daga yau Litini.

Yajin aikin dai ya biyo bayan taron da kwamitin zartarwa na kasa na kungiyar ta ASUU ya yi jiya Lahadi a jihar Ondo.

Kungiyar ta zargi gwamnatin Najeriya da gaza aiwatar da yarjejeniyar da suka kulla a baya game da yadda za a inganta yanayin aiki a jami'o'in kasar.

Yawaitar yajin aiki daga malaman jami'o''in na tasiri kan sha'anin ilimi a wannan kasa ta Najeriya, mafi yawan al'umma a Nahiyar Afrika.