Mafi Karancin Albashi: Kungiyoyin Kwadagon Nijeriya Sun Janye Yajin Aiki
(last modified Tue, 06 Nov 2018 05:23:25 GMT )
Nov 06, 2018 05:23 UTC
  • Mafi Karancin Albashi: Kungiyoyin Kwadagon Nijeriya Sun Janye Yajin Aiki

Kungiyoyin kwadago a Nijeriya sun sanar da janye yajin aikin gama garin da suka shirya fara yi a yau Talata bayan yarjejeniyar da suka cimma da masu ruwa da tsaki a kasar a daren jiya Litinin kan shawarwari biyu na mafi karancin albashin ma'aikata .

Shugaban kungiyar Kwadago ta Nijeriya din (NLC) Comrade Ayuba Wabba ne ya sanar da hakan a karshen wani taro na gaggawa da kwamitin bangarori uku da aka tsara don tattauna batun karin mafi karancin albashin ma'aikatan inda yace sun amince su dakatar da yajin aiki na gama garin ne bayan sun cimma yarjejeniya sannan kuma dukkanin bangarorin sun sanya hannu kanta.

Ita ma a nata bangaren shugabar kwamitin bangarori ukun Ms Amma Pepple ta ce a halin yanzu dai an cimma matsaya kan mafi karancin albashin, tana mai cewa a halin yanzu dai akwai adadin biyu da aka tsaya kai na Naira 24,000 na gwamnati da kuma  Naira 30,000 da 'yan kwadagon suka bukata a matsayin mafi karancin albashin, tana mai cewa a yau Talata kwamitin zai gabatar wa shugaba Muhammadu Buhari na Nijeriya rahoto kan abin da suka cimma din.

Kafin hakan dai kungiyoyin dai kungiyoyin kwadagon sun sanar da cewa za su fara yajin aiki na gama garin ne a yau Talata don sanar da rashin amincewarsu da albashin Naira 22, 500 da gwamnonin jihohin kasar suka sanar a matsayin mafi karancin albashi din suna masu cewa wannan adadin ya kasa.