Gwamnan Jihar Ebonyi Yayi Barazanan Ajiye Aikinsa Dangane Da Mafi Karancin Albashi
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i33989-gwamnan_jihar_ebonyi_yayi_barazanan_ajiye_aikinsa_dangane_da_mafi_karancin_albashi
Gwamnan jihar Ebonyi David Umahi ya yi barazanar ajiye aikinsa idan har mafi karancin albashi na naira dubu 30 ya tabbata
(last modified 2018-11-08T06:44:12+00:00 )
Nov 08, 2018 06:44 UTC
  • Gwamnan Jihar Ebonyi Yayi Barazanan Ajiye Aikinsa Dangane Da Mafi Karancin Albashi

Gwamnan jihar Ebonyi David Umahi ya yi barazanar ajiye aikinsa idan har mafi karancin albashi na naira dubu 30 ya tabbata

Kamfanin dillancin labaran NAN na Najeriya ya nakalto gwamnan yana fadar haka a jiya laraba a birnin Abakaliki babban birnin Jihar. Ya kuma kara da cewa kashi 95% na jihohin tarayyar Najeriya 36 ba zasu iya biyan naira dubu 30 a matsayin albashi mafi karanci ga ma'aikatansu ba. 

Umahi ya ce jihohi zasu iya biyan albashi mafi karanci na naira dubu 30 ne kadai, idan an sauya dokoki da tsarin rabon kudade na gwamnatin tarayyar kasar.

A halin yanzu, inji shi, gwamnatin tarayya ce take kwasar kashi 52% na kudaden shiga a kasar. Sannan idan an lissafa da ma'aikatan kananan hukumomi a jiharsa, ya ce dole ne gwamnatinsa ta karbi bashin naira biliyon guda ta hada da abinda take samu a kasonta na gwamnatin tarayyar, kafin ta iya biyan albashin ma'aikatan jihar.

Umahi ya ce ba zai zaman gwamnan jiha wacce zata ware kashi 100% na kudaden shigarta, ga biyan albashin ma'aikata ba. Har'ila yau gwamnan ya bukaci a sake nazarin batun tallafin da gwamnatin tarayyar take bawa man fetur a kasar, kamar yadda ita gwamnatin tarayya da kuma na jihohi suka bukata a baya.