Hatsarin Mota Ya Hallaka Mutum 47 A Kasar Zimbabwe
Akalla mutane 47 sun rasa rayukansu bayan wasu motocin safa biyu sun yi karo da juna a tsakanin birnin Harare da garin Rusape da ke yankin Kudu maso gabashin kasar Zimbabwe.
Kamfanin dillancin labaran Farana ya nakalto jami’an ‘yan sandan kasar Zimbabwe na cewa a jiya laraba wani hatsarin mota ya ci rayukan mutum 47 a kasar. tare da bayyana cewa ganin munin hatsarin ba za a iya wallafa hotunan hatsarin ba
Ana yawan samun hattsuran motoci a Zimbabwe saboda lalacewar hanyoyi bayan kwashe tsawon shekaru ba tare da kula da su ba.
Koda dai bayanai na cewa, a kwanan nan aka gyara hanyar da hatsarin baya-bayan ya auku.
A shekarar bara, an samu mutane 43 da suka rasa rayukansu a wani hatsarin mota a yankin arewacin kasar.