Hatsarin Mota Ya Hallaka Mutum 47 A Kasar Zimbabwe
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i33992-hatsarin_mota_ya_hallaka_mutum_47_a_kasar_zimbabwe
Akalla mutane 47 sun rasa rayukansu bayan wasu motocin safa biyu sun yi karo da juna a tsakanin birnin Harare da garin Rusape da ke yankin Kudu maso gabashin kasar Zimbabwe.
(last modified 2018-11-08T11:48:12+00:00 )
Nov 08, 2018 11:48 UTC
  • Hatsarin Mota Ya Hallaka Mutum 47 A Kasar Zimbabwe

Akalla mutane 47 sun rasa rayukansu bayan wasu motocin safa biyu sun yi karo da juna a tsakanin birnin Harare da garin Rusape da ke yankin Kudu maso gabashin kasar Zimbabwe.

Kamfanin dillancin labaran Farana ya nakalto jami’an ‘yan sandan kasar Zimbabwe  na cewa a jiya laraba wani hatsarin mota ya ci rayukan mutum 47 a kasar. tare da bayyana cewa ganin munin hatsarin ba za a iya wallafa hotunan hatsarin ba

Ana yawan samun hattsuran motoci a Zimbabwe saboda lalacewar hanyoyi bayan kwashe tsawon shekaru ba tare da kula da su ba.

Koda dai bayanai na cewa, a kwanan nan aka gyara hanyar da hatsarin baya-bayan ya auku.

A shekarar bara, an samu mutane 43 da suka rasa rayukansu a wani hatsarin mota a yankin arewacin kasar.