Madagaska : Rajoelina Ke kan Gaba A Zaben Shugaban Kasa
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i33996-madagaska_rajoelina_ke_kan_gaba_a_zaben_shugaban_kasa
Hukumar zabe mai zaman kanta a Madagaska ta fitar da sakamakon wucin gadi na zaben shugaban kasar, wanda ya nuna cewa dan takara Andry Rajoelina ne ke kan gaba a zaben da kashi 45,07% na yawan kuri'un da aka kada.
(last modified 2018-11-08T11:57:42+00:00 )
Nov 08, 2018 11:57 UTC
  • Madagaska : Rajoelina Ke kan Gaba A Zaben Shugaban Kasa

Hukumar zabe mai zaman kanta a Madagaska ta fitar da sakamakon wucin gadi na zaben shugaban kasar, wanda ya nuna cewa dan takara Andry Rajoelina ne ke kan gaba a zaben da kashi 45,07% na yawan kuri'un da aka kada.

Sakamakon da hukumar ta fitar a yau, ya kuma nuna cewa dan takara Marc Ravalomanana ke a matsayi na biyu da kashi (40,30%), sai dan takara  Hery Rajaonarimampianina wanda ya samu kashi 3,29%. 

Saidai tuni tsohon shugaban kasar wanda ya zo a matsayi na uku ya yi fatali da sakamakon zaben wanda a cewarsa na cike da kura kurai.

Wata sanarwa da Mista Rajaonarimampianina, ya fitar ta nuna cewa an samu matsaloli a zaben da suka hada da jinkiri wajen kai kayan zabe da walakanci sai kuma wasu kuri'u da aka riga aka sanya wa hannu.

Tunda farko dai hasashen da akayi ya nuna cewa zaben zai yi zafi tsakanin 'yan takara uku wadanda duk sananun fuskoki ne a wannan kasar ta Madagaska.