MDD Na Son A Dage Zaben Libiya Har Zuwa 2019
Nov 09, 2018 06:38 UTC
Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci da a dage zabe a kasar Libiya har zuwa shekara 2019 mai zuwa.
Wakilin MDD, a Libiya ya bayyana cewa za'ayi wani taron kasa a farkon shekara 2019, sannan a gudanar da zabe a kasar.
M. Ghassan Salame, ya bayyana wa kwamitin tsaro na MDD cewa taron zai baiwa 'yan Libiyar damar tattauna makomar kasarsu.
A watan Disamba mai zuwa na shekara 2018 din nan ne aka tsara za'a gudanar da zaben na Libiya.
Tags