Yan Sanda 334,000 Suke Kokarin Tabbatar Da Tsaro A Najeriya
Spetan yan sanda a tarayyar Najeriya Ibrahim Idris ya bayyana cewa yansanda kimani 334,000 ne suke aikin tabbatar da zaman lafiya da tsaro a kasar
Jaridar Punch ta Najeriya ta nakalto Spetan yansandan yana fadar haka a yau talata a wani taron koyawa yan makaranta shugabanci na gari.
Mr Olusegun Odumosu na babban hetkwatan yansandan kasar ne ya wakilci shugaban yansanda Ibrahim Idris a taron bada kyauta kan kwarewa a shugabanci na wannan shekara ta 2018..
Spetan yansandan ya ce matsalar garkuwa da mutane don karban kudaden fansa na daga cikin matsalolin tsaro da suke addabar kasar a halinn yanzu. Sannan makarantu a kasar na daga cikin wadanda suka fi kowa fuskantar wannan matsalar.
Daga karshe ya yi kira ga aka kafa jami'an tsarin sa kai a anguwanni don taimakawa yansanda a cikin aikinsu na tabbatar da tsaro a kasar.