Najeriya : Sojoji Sun Kama 'Yar Kunan Bakin Wake
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i34070-najeriya_sojoji_sun_kama_'yar_kunan_bakin_wake
Sojoji na runduna ta 251 a birnin Maiduri sun kama wata mata diyar shekara 19 a lokacinda take kokarin kai harin kunan bakin wake a bir Maidugu na jihar Borno a tarayyar Nageriya.
(last modified 2019-04-27T14:25:10+00:00 )
Nov 13, 2018 19:00 UTC
  • Najeriya : Sojoji Sun Kama 'Yar Kunan Bakin Wake

Sojoji na runduna ta 251 a birnin Maiduri sun kama wata mata diyar shekara 19 a lokacinda take kokarin kai harin kunan bakin wake a bir Maidugu na jihar Borno a tarayyar Nageriya.

Shafin yanar gizo na shara reporters a tarayyar Najeriya ya kara da cewa matar mai suna shaidatu Adamu ta ce ta fito ne daga garin Gwaza na jihar da Borno sannan ita kadai aka aika don aiwatar da aikin kunan bakin waje a birnin na Maiduguri.

Shaidatu ta kara da cewa ta zauna dajin sambisa na tsawon shekaru ukku. Sojojin sun gayyaci gwararru a rundunar kwance boma-bomai wadanda suka kwance mata damara suka kuma kaita bangaren bincike don karin tambayoyi.

Duk da cewa sojojin Najeriya sun sami nasarar kwace yankunan da mayakan Boko haram suke iko da shi a jihar Borno amma har yanzun sukan kai hare-hare kan kan jami'an tsaro da kuma farare hula daga lokaci zuwa lokaci.