Cece-kuce Kan Rashin Lafiyar Shugaba Ali Bongo A Gabon
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i34079-cece_kuce_kan_rashin_lafiyar_shugaba_ali_bongo_a_gabon
A Gabon, rashin jin duniyar shugaban kasar Ali Bongo Ondimba, yau kusa da mako uku ya tayar da zazzafar muhawara tsakanin 'yan kasar.
(last modified 2018-11-14T02:17:21+00:00 )
Nov 14, 2018 02:17 UTC
  •  Cece-kuce Kan Rashin Lafiyar Shugaba Ali Bongo A Gabon

A Gabon, rashin jin duniyar shugaban kasar Ali Bongo Ondimba, yau kusa da mako uku ya tayar da zazzafar muhawara tsakanin 'yan kasar.

Marabin da a ga shugaban kasar bainar jama'a tun a ranar 24 ga watan Oktoba da ya gabata, bayan da aka sanar da kwantar dashi a wani babban asibitin birnin Riyad na Saudiyya, wanda kuma yanzu haka ya sanya ake samun bayanai iri daban daban kan rashin lafiyar na shugaban kasar.

'Yan hamayya a kasar dai na a sahun gaba wajen neman gwamnatin kasar akan ta yi musu karin bayyani akan halin da shugaba Bongon yake ciki, bayan zargin gwamnatin da boye gaskiyar halin da shuguban yake ciki.

A cewar Alexandre Barro, jigo a wata jam'iyya ta kasar ya kamata gwamnati ta fito fili ta bayyana 'yan kasar hakikanin abunda yake faruwa.

Shi kuwa Paul Malékou, kakakin wani kawancen datijai a kasar, ya bukaci gwamnatin ta Gabon data bi duk hanyar data dace na kafa wani shirin wucin gadi cikin ruwan sanyi don tabbatar da kwanciyar hankali a kasar.

Ita kuwa jam'iyyar (UN) mai adawa a kasar zargin gwamnatin kasar ta yi da yin karya, bayan sanawar da fadar shugaban kasar ta fitar dangane da batun rashin lafiyar shugaba  Ali Bongon.

A ranar Lahadi data gabata ne kakakin fadar gwamnatin kasar, Ike Nguoni, ya sanar da cewa shugaban kasar ya fara murmurewa daga rashin lafiyar dake damunsa, saidai a cewar jam'iyyar ta UN, ya kamata a bayyana wa jama'ar kasar sakamakon yanayin rashin lafiyar shugaban wanda asibitin Riyad ya mika masu.

Haka zalika 'yan adawa sun bukaci fira ministan kasar, Emmanuel Issoze Ngondet, ya jagoranci wata tawagar 'yan kasar tare da wakilan jama'a zuwa birnin Riyad cikin gajeren lokaci domin ganawa da shugaban kasar da likitocinsa dama hukumomin na Saudiyya. 

Sanarwar da gwamnatin gabon ta fitar bata gamsar da jama'ar kasar ba, duk da amsa cewa lalle shugaban yana fama da rashin lafiya sosai.

Wasu dai na bukatar a nuna masu hoton shugaban kasar ko kuma a yi hira da shi, domin gamsar dasu akan batun.

Rashin jin duriyar shugaban kasar dai ya tayar da zazzafar muhawara tsakanin 'yan kasar a daidai lokacin da labarai mabanbamta ciki har da masu tayar da hankali ke yawo kan shafukan yada labarai dana sada zumunta. 

Wata majiya kusa da shugaban kasar ta bayyana cewa Ali Bongon na fama ne da ciwon bugun jini na kwakwaluwa, wanda ya sanya aka kwantar dashi asibiti na Riyad.

Shi dai shugaba Bongon ya je Saudiyya ne wajen halartar taron tattalin arzikin ''Davos'' da Saudiyya ta shirya a watan Oktoban da ya gabata.