Najeriya: Mutane 16 Sun Rasa Rayukansu Sakamakon hare-Hare Boko Haram
Kimanin mutane 16 ne aka tabbatar da sun rasa rayukansu sakamakon hare-haren mayakan kungiyar Boko Haram a cikin jahar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya.
Kamfanin dillancin labaran AFP ya habarta cewa, mayakan kungiyar ta Boko haram sun kaddamar da hare-hare a wasu yankuna da ke cikin jahar, inda daga ranar Litin zuwa yau laraba sun kashe mutane da dama inda ya zuwa yanzu an iya samu gawawwakin mutane akalla 16.
Rahoton ya ce mayakan sun kashe wani manomi a cikin gonarsa a kauyen Garimari da ke tazarar kilo mita 13 daga birnin Maiduguri, haka nan kuma an samu gawawwakin mutane 15 dukkaninsu 'yan kato da gora, wadanda aka kashe su a kauyukan Kaza Wadara da suke kusa da garin Mungunu.
Haka nan kuma rahoton ya kara da cewa, akwai mutanen da dama da ba a ji duriyarsu ba, kuma ba a san makomarsu ba, tun bayan da mayakan na Boko Haram suka kaddamar da hare-hare a ranar Litinin da ta gabata.