Majalisar Dinkin Duniya Ta Dauke Wa Eritrea Takunkumi
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i34094-majalisar_dinkin_duniya_ta_dauke_wa_eritrea_takunkumi
A zaman da kwamtin tsaron majalisar dinkin duniya ya gudanar, ya sanar da dauke wa kasar Eritrea takunkuman da aka dora mata.
(last modified 2018-11-14T15:58:24+00:00 )
Nov 14, 2018 15:58 UTC
  • Majalisar Dinkin Duniya Ta Dauke Wa Eritrea Takunkumi

A zaman da kwamtin tsaron majalisar dinkin duniya ya gudanar, ya sanar da dauke wa kasar Eritrea takunkuman da aka dora mata.

Kamfanin dillancin labaran Faransa ya bayar da rahoton cewa, a zaman da kwamitin majalisar dinkin duniya ya gudanar a yau, dukkanin mambobin kwamitin su 15 sun amince da dauke wa Eritrea takunkuman da aka kakaba mata.

Wannan mataki dai ya biyo kyautatar alaka da aka samu tsakanin Habasha da Eritrea ne tun a cikin watan Yulin da ya gabata, bayan kwashe shekaru fiye da 20 suna matsananciyar gaba, bisa takaddamar iyakokin da ke tsakaninsu.

A halin yanzu dai Eritrea da Jobouti suna tattaunawa domin warware matsalolin da ke tsakaninsu, inda firayi ministan kasar Habasha Abi Ahmad yake shiga tsakani domin sasanta kasashen biyu, yunkurin da majalisar dinkin duniya suka yi lale marhabin da shi.

 A cikin shekara ta 2009 ce kwamitin tsaron majalisar dinkin duniya ya kakaba ma Eritrea takunkumai, bisa zarginta da taimaka ma 'yan kungiyar Al-shahab na Somalia, zargin da Eritrea take musuntawa.