'Yan Takara A Madagaska Sun Yi Watsi Da Sakamakon Zabe
'Yan takara uku a zaben shugaban kasa na Madagaska sun nuna shakku dangane da sakamakon wucin gadi da hukumar zaben kasar mai zaman kanta (CENI) ta fitar.
A yayin da bangaren shugaba mai barin gado, Hery Rajaonarimampianina, ke cewa an samu tarin matsaloli a zaben, shi kuwa bangaren tsohon shugaban wucin gadi na kasar, Andry Rajoelina, kalubalantar sakamakon zaben ya yi tare da janye wa daga sanya ido a kidayar kuri'un.
A nasa bangare kuwa kwamitin goyan bayan tsohon shugaba Marc Ravalomanana, na korafi ne akan yadda hukumar zaben ta CENI ta ki bawa jam'iyyarsu damar duba sakamakon na ko wacce runfar zabe.
Sakamakon wucin gadin da hukumar zaben kasar ta fitar dai, ya kunshi kashi 60 cikin dari na yawan kuri'un da aka kada, wanda ya nuna a yanzu dan takara Andry Rajoelina ke kan gaba da 39% a yayin da shi kuwa babban abokin hammayarsa tsohon shugaba Marc Ravalomanana ya samu kashi 37%.
Hukumar zaben kasar dai ta ce zaben ya gudana cikin haske inda dukkan wakilan 'yan takara suka samu damar duba duk bayannan da suka bukata, amma bangaren shugaba mai barin gado Hery Rajaonarimampianina na ci gaba da zargin hukumar da rshin tsara zaben yadda ya kamata.