Gabon : An Amince Mataimakin Shugaban Kasa Ya Jagoranci Taron Majalisar Ministoci
Kotun tsarin mulki a Gabon ta amince mataimakin shugaban kasar ya kira tare da jagorantar taron majalisar ministocin kasar a yayin da aka shiga mako na uku na jinyar da shugaban kasar ke yi a wani asibitin Riyad.
Hakan dai ya biyo bayan bukatar da fira ministan kasar Emmanuel Issoze Ndondet ya gabatar.
Kotun tsarin mulki ta amince da hakan ne bayan yiwa wata ayar doka mai lamba 13 karin sakin layi, akan batun rashin tafiyar da mulki ko rashin samun dama daga daga shugaban kasa.
kafin dai a amince shugaban gwamnati ko mataimakin shugaban kasa ya tafiyar da wasu harkokin mulki na shugaban kasa dole sai fira minista ko kashi guda cikin goma na majalisar ministoci sun gabatar da bukata gaban kotun tsarin mulkin kasar.
kafin yiwa kundin tsarin mulkin kasar 'yar kwaskwarima, shugaban kasar ne kawai yake da karfin ikon bada dama ga mataimakinsa ya shirya taron majalisar ministoci.
A Gabon dai an shafe mako uku ba tare da gudanar da taron majalisar ministocin kasar na mako mako ba.
Rashin jin duriyar shugaba Ali Bongo tun a ranar 24 ga watan Oktoba da ya gabata, ya tayar da zazzafar muhawara tsakanin 'yan kasar musamman kan labarai mabanbamta marasa dadi dake yako a shafukan yada labarai.