Za'a Je Zagaye Na Biyu A Zaben Madagaska
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i34142-za'a_je_zagaye_na_biyu_a_zaben_madagaska
A Madagaska, za'a fafata a zagaye na biyu na zaben shugaban kasar tsakanin dan takara Andry Rajoelina da kuma Marc Ravalomanana.
(last modified 2018-11-18T06:41:23+00:00 )
Nov 18, 2018 06:41 UTC
  • Za'a Je Zagaye Na Biyu A Zaben Madagaska

A Madagaska, za'a fafata a zagaye na biyu na zaben shugaban kasar tsakanin dan takara Andry Rajoelina da kuma Marc Ravalomanana.

Sakamakon da hukumar zaben kasar mai zaman kanta ta fitar, ya nuna cewa dan takara Andry Rajoelina kan gaba da kashi (39,19%) da Marc Ravalomanana da kashi (35,29%). 

A ranar 19 ga watan Disamba mai zuwa ne za'a gudanar da zaben a zagaye na biyu.

Nan da ranar 26 ga watan Nowamba ne kotun tsarin mulkin kasar zata bayyana matsayinta akan sakamakon zaben.