Ban Da Niyyar Sake Tsayawa Takara_Mohamed Ould Abdel Aziz
Shugaban Kasar mauritania, Mohamed Ould Abdel Aziz, ya ce bai da niyyar sake tsayawa takara a zaben shugaban kasar na 2019 domin neman wani wa'adin mulki a karo na uku.
Shugaba Ould Abdel Aziz, ya bayyana hakan ne a yayin da yake halartar wani taron birane masu tarihi a yankin Oualata dake kudancin kasar.
Mohamed Ould Abdel Aziz ya ce zai mutunta kundin tsarin mulkin kasar, duk da a cewarsa yana jin kiraye kiraye da magoya bayansa ke yi na ya sake tsayawa takara.
A game da batun tsaro a yankin kuwa shugaba Mohamed Ould Abdel Aziz, ya tabo batun rundinar hadin gwiwa nan ta G5 Sahel, wacce a cewarsa har yanzu take fuskantar tsaiko wajen fara aiki gadan gadan.
A ranar 6 ga watan Disamba mai zuwa ne kasar Mauritania zata karbi bakuncin wani taron neman tallafi na kungiyar ta G5 Sahel data kunshi kasashen, (Burkina Faso, Mali Nijar, Mauritania da kuma Chadi) da aka kafa domin yaki da ta'addanci da safara mutane da kwayoyi a yankin na Sahel.