An Fara Yakin Neman Zabe A D.R Congo
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i34185-an_fara_yakin_neman_zabe_a_d.r_congo
A Jamhuriyar Demokuradiyyar Congo a cikin daren yau Larabe ne da misalin karfe 12 na dare, za'a fara yakin neman zaben shugaban kasar.
(last modified 2018-11-21T14:45:40+00:00 )
Nov 21, 2018 14:45 UTC
  • An Fara Yakin Neman Zabe A D.R Congo

A Jamhuriyar Demokuradiyyar Congo a cikin daren yau Larabe ne da misalin karfe 12 na dare, za'a fara yakin neman zaben shugaban kasar.

Da yake sanar da hakan shugaban hukumar zaben kasar, (CENI), Corneille Nangaa, ya yi fatan ''Allah ba mai rabo sa'a'', tare da kira ga 'yan siyasar kasar dasu kai zuciya nesa su gudanar da yakin neman zaben cikin kwanciyar hankali da lumana.

'Yan takara 21 ne dai zasu fafata a zaben na ranar 23 ga watan Disamba mai zuwa, domin maye gurbin shugaban kasar mai barin gado Joseph Kabila, wanda ya shafe shekara 18 kan madafun ikon kasar tun bayan rasuwar mahaifinsa tsohon shugaba Laurent-Désiré Kabila a shekara 2001.

Shugaban kasar mai barin gado, Joseph Kabila, ya dai janye daga takara zaben ne biyo fuskantar matsin lamba daga kasashen duniya da 'yan adawa na kasar, akan kada ya sake tsayawa takara saboda kundin tsarin mulkin kasar ya haramta masa da hakan.

Sama da 'yan kasar ta Jamhuriyar D Congo miliyan 40 ne da suka cancanci zabe ne zasu kada kuri'a a zaben a cewar hukumar zaben kasar mai zaman kanta, duk da cewa akwai 'yan kasar da dama musamman daga bangaren adawa dake korafi kan yadda zaben zai gudana wanda za'a gudanar dashi ta na'urar zabe.