An Fara Yakin Neman Zabe A D.R Congo
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i34193-an_fara_yakin_neman_zabe_a_d.r_congo
Yau Alhamis an fara yakin neman zaben shugaban kasa a Jamhuriyar Demokuradiyyar Congo.
(last modified 2018-11-22T07:24:27+00:00 )
Nov 22, 2018 07:24 UTC
  • An Fara Yakin Neman Zabe A D.R Congo

Yau Alhamis an fara yakin neman zaben shugaban kasa a Jamhuriyar Demokuradiyyar Congo.

Da yake sanar da hakan shugaban hukumar zaben kasar, (CENI), Corneille Nangaa, ya yi fatan ''Allah ba mai rabo sa'a'', tare da kira ga 'yan siyasar kasar dasu kai zuciya nesa su gudanar da yakin neman zaben cikin kwanciyar hankali da lumana.

'Yan takara 21 ne dai zasu fafata a zaben na ranar 23 ga watan Disamba mai zuwa, domin maye gurbin shugaban kasar mai barin gado Joseph Kabila, wanda ya shafe shekara 18 kan madafun ikon kasar tun bayan rasuwar mahaifinsa tsohon shugaba Laurent-Désiré Kabila a shekara 2001.

Shugaban kasar mai barin gado, Joseph Kabila, ya dai janye daga takara zaben ne biyo bayan fuskantar matsin lamba daga kasashen duniya da 'yan adawa na kasar, akan kada ya sake tsayawa takara saboda kundin tsarin mulkin kasar ya haramta masa da hakan.