Boko Haram Ta Sace Mutum 50 A Najeriya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i34199-boko_haram_ta_sace_mutum_50_a_najeriya
Rahotanni daga Najeriya na cewa, wasu da ake kyautata zaton mayakan Boko Haram ne sun sace wasu 'yan kauye 50 a iyakar kasar da Jamhuriya Kamaru.
(last modified 2018-11-23T05:07:25+00:00 )
Nov 23, 2018 03:24 UTC
  • Boko Haram Ta Sace Mutum 50 A Najeriya

Rahotanni daga Najeriya na cewa, wasu da ake kyautata zaton mayakan Boko Haram ne sun sace wasu 'yan kauye 50 a iyakar kasar da Jamhuriya Kamaru.

Mutanen dai 'yan kauye ne da suka shiga gandun daji domin neman itacen dafuwa.

Da yake tabbatar da hakan ga kamfanin labaren AFP, shugaban 'yan kato da gora dake taimakawa sojoji a yaki da Boko Haram na yankin, Umar Kachalla, ya ce a ranar Asabar data gabata mayakan na Boko Haram sun tattara mutane tare da yin awan gaba dasu, kuma tun lokacin ba'a sake samun labarinsu ba.

An samu labarin ne daga wajen wasu biyu daga cikin mutanen da suka kubuta daga hannun mayakan.

Bayanai sun nuna cewa wannan ba shi ne karon farko ba da irin hakan take faruwa a wannan yankin da ya kunshi gandun daji Wulgo da kuma gewayen dajin Gamboru, tun bayan da sojoji kasar suka tabbatar wa jama'a cewa sun murkushe kungiyar Boko haram a wanan yankin.