Najeriya : Zamu Kawo Gyara A Yaki Da Boko Haram_Buhari
Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya, ya ce gwamnatinsa za ta kawo gyara a yakin da take da kungiyar Boko Haram.
Wannnan dai na kunshe a cikin wata sanarwa da Garba Shehu, mai bai wa shugaban kasar shawara kan harkokin wasa labarai ya fitar inda kuma shugaban kasar ya bayyana matukar damuwarsa game da kisan da 'yan Boko Haram sukayi wa wasu sojin kasar a kauyen Metele da ke jihar Borno.
Sanarwar ta ce gwamnati za ta dauki kwararen matakai cikin gaggawa wajen ganin ba a sake maimaita kuskuren da akayi ba.
Gwamnatin ta kuma ce nan gaba za'a tattaunawa da manyan sojojin kasar da jami'an kleken asiri akan irin matakan da za'a dauka.
Rahotanni daga kasar dai sun nuna cewa sama da sojoji dari ne aka kashe a makwannin da suka gabata a garin na Metele dake jihar Borno a arewa maso gabashin kasar, saidai har yanzu rundinar sojin kasar bata tabbatar da adadin ba.