Nutsewar Jirgin Ruwa Ta Yi Ajalin Mutum 29 A Uganda
'Yan sanda a Uganda, sun tabbatar da mutuwar mutum 29 biyo bayan nutsewar wani jirgin ruwa a tafkin Victoria.
Jirgin ruwan dake dauke da mutum 100 ya nutse ne a ranar Asabar dauke da mutum 100 a kusa da Kampala babban birnin Kasar.
A cewar 'yan sanda an yi nasara ceto sama da mutum 20, amma akwai wani adadi na mutanen da suka bata.
Kakakin 'yan sanda kasar, Patrick Onyango, ya shaida wa kamfanin dilancin labarai na Reuters cewa, jirgin ya nutse ne sanadin lodi fiye da kima da kuma rashin kyawon yanayi.
Wannan dai ba shi ne karo na farko ba da ake samun hatsari jirgin ruwa a wannan tafkin Victoria, don ko a watan Satumba da ya gabata gomman mutane ne suka rasa rayukansu a wani hatsarin jirgin ruwa a gabar ruwan Tanzania.