Ziyarar Idriss Deby A Isra'ila, Ta Bar Baya Da Kura A Chadi
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i34243-ziyarar_idriss_deby_a_isra'ila_ta_bar_baya_da_kura_a_chadi
A Chadi ziyarar da shugaban kasar ne Idriss Deby Itmo, ya kkai a Israila ta bar baya da kura, inda wasu 'yan kasar ke aza ayar tambaya akan manufar ziyarar da kuma ko mahukuntan yahudawan ne suka bukace ta ko kuma na Chadi.
(last modified 2018-11-26T11:01:01+00:00 )
Nov 26, 2018 11:01 UTC
  • Ziyarar Idriss Deby A Isra'ila, Ta Bar Baya Da Kura A Chadi

A Chadi ziyarar da shugaban kasar ne Idriss Deby Itmo, ya kkai a Israila ta bar baya da kura, inda wasu 'yan kasar ke aza ayar tambaya akan manufar ziyarar da kuma ko mahukuntan yahudawan ne suka bukace ta ko kuma na Chadi.

A Jiya ne dai Mista Deby ya isa Isra'ila, a ziyarar data kasance ta farko ta wani shugaban kasar Chadi a kusa da shekara 50.

A yayin ganawar shuwagabannin biyu, fira ministan Isra'ila Benjamin Netanyahu, ya bayyana ziyarar da mai matukar tarihi.

Bayanai sun nuna cewa Isra'ilar ba tada hulda da Chadi tun a shekara 1972.