An Cafke Wasu Mayakn Al-shabab 8 A Kasar Somalia
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i3427-an_cafke_wasu_mayakn_al_shabab_8_a_kasar_somalia
Jami'an tsaron kasar Somalia sun cafke wasu mayakan kungiyar Al-shabab guda 8 a birnin magadishou a jiya.
(last modified 2018-08-22T06:58:05+00:00 )
Apr 04, 2016 23:06 UTC
  • An Cafke Wasu Mayakn Al-shabab 8 A Kasar Somalia

Jami'an tsaron kasar Somalia sun cafke wasu mayakan kungiyar Al-shabab guda 8 a birnin magadishou a jiya.

Kamfanin dillancin labaran Xin Huwa ya bayar da rahoto daga birnin Magadishou cewa, jami'an tsaron kame mutanen 8 ne bayan kai wani samame a wani gida da suke a cikin birnin, bayan samun bayanai na sirri dangane da kai komon da suke yi a wurin, an samu tarin makamai da motoci na kai hare-hare a inda suke.

Wannan samame dai ya zo kwana daya bayan wani hari da mayakan na Al-shabab masu dauke da akidar kafirta musulmi suka kai kan jami'an tsaro, inda suka kashe 5 daga cikinsu, da suka hada da wani babban jami'in tsaro na kasar ta Somalia.