Takunkumi Bai Hana Shigar Da Makamai A Sudan Ta Kudu Ba
Nov 29, 2018 10:04 UTC
Kungiyar (Conflict Armament Research) ta Birtaniya, ta fitar da wani rahoto wanda ke cewa takunkumin da aka kakaba wa Sudan ta Kudu kan makaman yaki bai yi wani tasiri ba.
Rahoton da kungiyar ta (CAR) a takaice, dake bincike kan rikice rikicen dake faruwa ta hanyar makaman yaki a duniya, ya ce takunkumin da aka kakaba wa Sudan ta Kudu dake fama da yakin basasa tun cikin shekara 2013, bai hana shigar da makaman yaki a kasar ba.
A binciken tsawan shekaru hudu data gudanar kungiyar ta (CAR), ta bayyana yadda aka yi ta samun safara makamai cikin Sudan ta Kudun daga wasu kasashe makobtanta.
Kasashen da rahoton ya zayyana sun hada da Uganda da Amurka da kuma wasu na Turai.
Tags