Gabon : Ali Bongo Ya Fara Jinya A Morocco
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i34277-gabon_ali_bongo_ya_fara_jinya_a_morocco
Rahotanni daga Morocco na cewa Shugaba Ali Bongo Ondimba na Gabon ya isa birnin Rabah, da sanyin safiyar yau Alhamis, inda zai ci gaba da jinya, bayan da ya bar kasar Saudiyya inda ya kwashe sama da wata guda na jinya.
(last modified 2018-11-29T07:34:21+00:00 )
Nov 29, 2018 07:34 UTC
  • Gabon : Ali Bongo Ya Fara Jinya A Morocco

Rahotanni daga Morocco na cewa Shugaba Ali Bongo Ondimba na Gabon ya isa birnin Rabah, da sanyin safiyar yau Alhamis, inda zai ci gaba da jinya, bayan da ya bar kasar Saudiyya inda ya kwashe sama da wata guda na jinya.

Har kawo yanzu babu wani hoton bidiyonsa da aka fitar na lokacin da ayek barin Saudiyya ko kuma na isa Moroccon, amma wata majiyar Diflomatsiyya a Morocco ta shaida isarsa kasar.

Duk da cewa dai har yanzu gwamnatin ta Gabon bata fayyace ainahin ciwan dake damun shugaban mai shekaru 59 ba, amma wasu majiyoyin sun ce Ali Bango na fama ne da matsalar kwakwaluwa.