Al'ummar Zimbabwe Sun Gudanar Da Zanga-Zangar Kin Jinin Gwamnati A Kasar
Dubun dubatan al'ummar kasar Zimbabwe musamman masu adawa da gwamnatin kasar sun gudanar da wata zanga-zanga a babban birnin kasar, Harare don nuna rashin amincewarsu da matsalolin tattalin arziki da ake fuskanta a kasar musamman karancin kayayyakin bukatun yau da kullum cikin har da man fetur.
Kamfanin dillancin labaran Hukumar Gidan Radio da Talabijin na Iran ya bayyana cewar masu zanga-zangar dai suna dauke ne da kwalaye da aka yi rubutun nuna rashin amincewa da salon mulkin shugaban kasar, Emmerson Mnangagwa, inda wasu suke bukatar da yayi murabus.
Zanga-zangar wacce aka gudanar da ita a jiya Alhamis, ita ce zanga-zangar kin jinin gwamnati ta farko da aka gudanar tun bayan rikicin da ya barke a kasar bayan zaben shugaban kasa a ranar 1 ga watan Augusta inda mutane kimanin 6 suka rasa rayukansu.
Jagoran 'yan adawan kasar Nelson Chamisa wanda kuma ya jagoranci masu zanga-zangar ya ce a baya sun hada karfi waje guda ne da nufin kawar da tsohon shugaban kasar Robert Mugabe ne don su sami sauyin rayuwa amma a halin yanzu tsananin da ake ciki ya fi na lokacin na sa. Don haka yayi kiran shugaban da yayi murabus.