Gabon : Ali Bongo Ya Bayyana A Karon farko Bayan Doguwar Jinya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i34318-gabon_ali_bongo_ya_bayyana_a_karon_farko_bayan_doguwar_jinya
A Karon farko tun bayan da ya fara jinya yau sama da wata guda, shugaban kasar Gabon Ali Bongo Odinba, ya bayyana a wani hoto a kasar Morocco inda ya je domin ci gaba da jinya bayan ya bar Saudiyya.
(last modified 2018-12-03T23:44:35+00:00 )
Dec 03, 2018 23:44 UTC
  • Gabon : Ali Bongo Ya Bayyana A Karon farko Bayan Doguwar Jinya

A Karon farko tun bayan da ya fara jinya yau sama da wata guda, shugaban kasar Gabon Ali Bongo Odinba, ya bayyana a wani hoto a kasar Morocco inda ya je domin ci gaba da jinya bayan ya bar Saudiyya.

Kafofin yada labarai da dama daga Morocco, sun wallafa hoton shugaban a wani asibitin soji dake birnin Rabat, a yayin sarkin Morocco Mohammad na VI na ya kai masa ziyara. 

Hoton dai na nuna Shugaba Bongo sanye da kayan gargajiya na Morocco gami da rawani a kansa, a cikin raha.

Nuna wannan hoton dai ya kawo karshen kace-nace da ake yi a kasar ta Gabon na cewa shugaban mai shekaru 59 na cikin mawuyacin hali.

A  ranar 24 ga watan Oktoba da ya gabata ne Shugaban Ali Bongo ya kamu da rashin lafiya a Saudiyya a yayin da yake halartar wani taron tattalin arziki a birnin Riyad, bayan hakan ne a makon da ya gabata ya bar Saudiyya zuwa Morocco domin ci gaba da jinya.