Najeriya : EFCC Ta Bukaci Gurfanar Da Tsohuwar Ministar man Fetur
Hukumar yaki da cin hanci dakarbar rashawa ta (EFCC), a Najeriya ta fitar da sammacin kame tsohuwar ministar man fetur ta kasar, Diezani Alison-Madueke, domin ta gurfana a gaban kotu kan zargin rubda-ciki da milyoyin daloli na al'ummar kasar.
Wata sanarwa da hukumar ta (EFCC), ta fitar, ta ce yau Talata za'a gabatar da takardar sammacin tsohuwar ministar domin tiso keyarta zuwa kasar daga birnin Landon inda take da zama.
Sanarwar ta kara da cewa kotu na bukatar tsohuwar ministar da kuma wani makusancinta hamshakin dan kasuwa su bayyana gabanta a ranar 25 ga watan Fabrairu mai zuwa kan zargin amfani da dukiyar kasa ta hanyar da bata dace ba da kuma cin hanci da karbar rashawa.
Hukumar ta EFCC, ta ce ta dauki dukkan matakan da suka dace na ganin tsohuwar ministar ta gurfana a gabanta.
Diezani Alison-Madueke, wace ta rike mukamin ministar man fetur a karkashin mulkin tsohon shugaban kasar Goodluck Jonathan, kuma macce ta farko data rike mukamin shugabar kungiyar kasashe masu arzikin man fetur a duniya (OPEC), ana zarginta da hallata kudaden haramu da karbar rashawa a kasashen da suka hada da AMurka, Biritaniya, Italiya da kuma Najeriya.