An Sake Sa Ranar Sake Zama Tsakanin Gwamnati Da Malaman Jami'oin Nijeriya
An sanar da ranar Litinin mai kamawa, 10 ga watan Disamba, a matsayin ranar da za a sake zama teburin tattaunawa tsakanin gwamnatin tarayyar Nijeriya da Kungiyar Malaman Jami'oi na kasar ASUU a kokarin da ake yi na kawo karshen yajin aikin da malaman suke ci gaba da yi.
Ministan kwadago da ayyuka na Nijeriya, Chris Ngige, ce ya sanar da hakan cikin wata sanarwa da ya fitar dauke da sanya hannun daraktan watsa labarai na ma'aikatar, Samuel Olowookere, inda ya ce bangarori biyun za su zauna a teburin tattaunawar a ranar Litinin din da misalin karfe 4 na yamma a ma'aikatar kwadago da ayyuka din don tattauna hanyoyin da za a kawo karshen yajin aiki.
Sabuwar tattaunawar da za a yi din dai tana zuwa ne 'yan kwanaki bayan da gwamnatin Nijeriyan ta sanar da hukumomin jami'on kasar kan wata doka da suka kafa na hana duk wani malamin da bai koma bakin aikinsa albashinsa, lamarin da kungiyar malaman jami'oin suka ce hakan ba zai hana su ci gaba da neman hakkokinsu ba.
A shekaran jiya ma dai bangarori biyun sun tattauna kan batun yajin aikin sai dai ba su cimma matsaya ba.
Malaman jami'oin dai sun shiga yajin aikin ne sakamakon abin da suka kira gazawar gwamnatin wajen cika alkawurran da aka yi musu na kyautata rayuwarsu tun zamanin gwamnatocin da suka shude.