Kungiyar G5 Sahel, Ta Samu Alkawalin Kudaden Da Take Bukata
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i34356-kungiyar_g5_sahel_ta_samu_alkawalin_kudaden_da_take_bukata
Masu hannu da shunu da abokan hulda na kungiyar G5 Sahel, sun alkawarta bai wa kungiyar tallafin kudade kusa da Biliyan biyu na Yuro da kungiyar ke bukata domin aiwatar da wasu shirye shiryenta na ayyukan ci gaba domin yaki da mayakan dake ikirari da sunan jihadi.
(last modified 2018-12-07T01:13:54+00:00 )
Dec 07, 2018 01:13 UTC
  • Kungiyar G5 Sahel, Ta Samu Alkawalin Kudaden Da Take Bukata

Masu hannu da shunu da abokan hulda na kungiyar G5 Sahel, sun alkawarta bai wa kungiyar tallafin kudade kusa da Biliyan biyu na Yuro da kungiyar ke bukata domin aiwatar da wasu shirye shiryenta na ayyukan ci gaba domin yaki da mayakan dake ikirari da sunan jihadi.

Da yake sanar da hakan ga manema labarai bayan taron neman tallafi na kungiyar a Mauritania, shugaban kungiyar a wannan karo, kana shugaban kasar Nijar, Mahamadou Issoufou, ya ce wannan alkawarin zai cike ma kungiyar gibi dukkan bukatunta.  

Kungiyar G5 Sahel, wacce ta kunshi kasashen (Mali, Burkina Faso, Chadi, Mauritania da kuma Jamhuriya Nijar), ta sanar cewa tana bukatar samun tallafin akalla yuro biliyan 1 da miliyan dari 9 don kammala ayyukan data sanya a gaba wajen yakar ‘yan ta’adda da safara mutane da miyagun kwayoyi a yankin Sahel.