An hallaka daya daga cikin shugabanin kungiyar Ashabab a Somaliya
Apr 05, 2016 03:51 UTC
Amurka ta sanar da hallaka daya daga cikin shugabanin kungiyar Ashabab a kasar Somaliya
Jaridar Le Figaro ta kasar Faransa ta habarta cewa yayin wani hari da jiragen saman yakin Amurka suka kai kasar Somaliya, an hallaka Hasan Ali Dura daya daga cikin shugabanin kungiyar Ashabab a Somaliya.
Ma'aikatar tsaron Amurka ta ce Hasan Ali Doura na daga cikin manya -manyan shugabanin kungiyar ta'addancin nan ta Ashabab mai alakar kut da kut da kungiyar Alka'ida.
Hasan Ali Dura na daga cikin wadanda suka shirya harin ta'addancin da a aka kai Otel Mukrim ta birnin magadushu a ranar 27 ga watan Maris din shekarar 2015 da ta gabata, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane 15.
Tags