Najeriya : An Cimma Yarjejeniyar Zaman Lafiya A Zaben 2019
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i34409-najeriya_an_cimma_yarjejeniyar_zaman_lafiya_a_zaben_2019
A Najeriya, yayin da babban zaben kasar ke karatowa, wata yarjejeniya ce ta zaman lafiya aka cimma tsakanin jam'iyyun siyasa, domin samar da zaman lafiya a yayin zaben na 2019 da kuma bayansa.
(last modified 2019-04-27T14:25:10+00:00 )
Dec 12, 2018 05:02 UTC
  • Najeriya : An Cimma Yarjejeniyar Zaman Lafiya A Zaben 2019

A Najeriya, yayin da babban zaben kasar ke karatowa, wata yarjejeniya ce ta zaman lafiya aka cimma tsakanin jam'iyyun siyasa, domin samar da zaman lafiya a yayin zaben na 2019 da kuma bayansa.

Dan takarar jam'iyyar APC mai mulki shugaba Muhammadu Buhari da wasu 'yan takara da dama sun sanya hannu a yarjejeniyar.

An cimma yarjejeniyar ce karkashin wani kwamitin zaman lafiya na kasa da tsohon shugaban kasar Janar mai ritaya Abdussalam Abubakar ke jagoranta.

Saidai jam'iyyar PDP mai adawa a kasar, ta kaurace taron, wanda daga bisani ta ce babu wata gayyatar taron da dan takaranta, Alhaji Atiku Abubakar, ya samu daga wannan kwamitin. 

Taron ya samu halartar malaman addinai da sarakunan gargajiya da kuma jakadu na kasashen ketare.

Dama dai an taba cimma irin wannan yarjejeniya ta zaman lafiya a zaben kasar na 2015, wanda kuma shi ne karon farko a tarihin kasar da wani dan takara na adawa ya kada jam'iyya mai mulki.