Najeriya/Zaben 2019 : Atiku Ya Sanya Hannu Kan Yarjejeniyar Zaman Lafiya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i34423-najeriya_zaben_2019_atiku_ya_sanya_hannu_kan_yarjejeniyar_zaman_lafiya
Dan takarar babbar Jam'iyyar adawa ta PDP a Najeriya, Alhaji Atiku Abubakar, ya sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a yayin zaben kasar na 2019 dama bayansa.
(last modified 2018-12-13T10:53:19+00:00 )
Dec 13, 2018 10:53 UTC
  • Najeriya/Zaben 2019 : Atiku Ya Sanya Hannu Kan Yarjejeniyar Zaman Lafiya

Dan takarar babbar Jam'iyyar adawa ta PDP a Najeriya, Alhaji Atiku Abubakar, ya sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a yayin zaben kasar na 2019 dama bayansa.

Alhaji Atiku Abubakar ya sanar da hakan ne a shafinsa na Twitter, da yammacin jiya Laraba.

Tsohon mataimakin shugaban kasa a Najeriyar, kana babban abokin hammaya na shugaban kasar Muhammadu Buhari, bai halarci taron sanya hannu kan yarjejeniyar ba a yayin taron da aka shirya a ranar Talata data gabata ba.

Samar da kwanciyar hankali a yayin zabuka a shi ne kusan babban abunda ake bukata a wannan kasa ta Najeriya, inda rikice-rikice masu nasaba da kabilanci da addini ke haddasa zaman dar-dar a yayin zabuka.