AU Ta Yi Allawadai Da Cin Zarafin Mata A Sudan Ta Kudu
Kungiyar tarayyar Afrika AU, ta fitar da wata sanarwa inda ta yi Allawadai da cin zarafin mata da 'yan mata ta hanyar lalata da su a Sudan ta kudu.
A sanarwar data fitar, wakiliyar musamman mai kula da tsaro da zaman lafiyar mata ta kungiyar AU, Mme Bineta Diop, ta sanar da cewa, rahotannin baya bayan nan sun nuna cewa kimanin mata da 'yan mata 150 ne aka yi wa fyade da kuma dukansu a garin Bentiu dake Sudan ta kudu.
Mme. Diop, ta bukaci masu ruwa da tsaki da su kai daukin gaggawa domin ceto matan da aka ci zarafinsu ta hanyar lalata a Sudan ta kudun.
Tun bayan barkewar yakin basasa a watan Disambar shekarar 2013 a Sudan ta kudu, an yi kiyasin dubban mutane ne rikicin ya yi ajalinsu, kana wasu Miliyan hudu tashin hankalin ya raba su da matsugunansu.