Najeriya Ta Shigar Da Kara Don Hukunta Kamfanonin Shell Da Eni
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i34425-najeriya_ta_shigar_da_kara_don_hukunta_kamfanonin_shell_da_eni
Gwamnatin Najeriya ta bada sanarwan cewa ta shigar da kara a gaban wata kotu na neman dalar Amurka biliyon 1.1 Daga Kamfanonin hakar man fetur na Royal Dutch Shell da Kuma Eni a birnin lodon na kasar Britania a yau Alhamis
(last modified 2018-12-13T18:59:47+00:00 )
Dec 13, 2018 18:59 UTC
  • Najeriya Ta Shigar Da Kara Don Hukunta Kamfanonin Shell Da Eni

Gwamnatin Najeriya ta bada sanarwan cewa ta shigar da kara a gaban wata kotu na neman dalar Amurka biliyon 1.1 Daga Kamfanonin hakar man fetur na Royal Dutch Shell da Kuma Eni a birnin lodon na kasar Britania a yau Alhamis

Kamfanin dillancin labaran reuters ya ce karar ta sayan filin hakar man fetur mai lamba OPL 245 ne wanda kamfaninin biyu suka yi a shekara ta 2011.

Labarin ya kara da cewa karar tana tuhumar wasu shuwagabannin kamfanonin da taimakawa wajen habaka cin hanci da rashwa a tsakanin jami'an gwamnatin Najeriya.

Mai shigar da kara kan shari'ar ya ce ana zargin kamfanonin biyu da bada cin hanci na dalar Amurka biliyon 1.1 don samun lasisin hakar man fetur a fili mai lamba OPL 245, amma don rikicin da ya taso daga baya har yanzun kamfanonin basu fara aikin hakar man ba.

Amma wakilin kamfanin dillancin labaran reuters ya ce  ya kasa samun jawabi daga ofishin alkalin alkalai na kasa dangane da wannan labarin har zuwa lokacin hada wannan rahoton.

Sai kuma kamfanin Shell ya bayyana cewa lasisin da ya samu na fili mai lamba OPL 245 yana da inganci kuma an yi shi bisa doka , kamar yadda ya dace.