An Tabbatar Da Laifin Kisa Kan Wani Tsofon Jami'in 'Yansandan Kasar Kenya
(last modified Thu, 13 Dec 2018 19:01:32 GMT )
Dec 13, 2018 19:01 UTC
  • An Tabbatar Da Laifin Kisa Kan Wani Tsofon Jami'in 'Yansandan Kasar Kenya

Alkalin wata babban kotu a kasar Kenya ya tabbatar da laifin kisa kan wani tsohon jami'in 'yansanda na kasar, hukuncin da kungiyoyin kare hakkin bil'adama suka yi na'am da shi.

Kamfanin dillancin labaran reuters ya bayyana cewa kotun ta tabbatar da cewa Nahashon Mutua yana da hannun cikin kissan Martin Koome a cikin dakin da ake tsare da shi a lokacinda jami'in dan sandan yake aiki a wani lokaci a shekara ta 2013.

Alkalin babban kotun Justice Stella Mutuku ya ce ya tabbatar ba tare da wani kwokwanto ba kan cewa Martin Koome ya mutu ne sanadiyyar raunukan da ya ji saboda azantarwa da aka yi masa a inda ake tsare da shi. 

A karshen zaman kotuna yau Alhamis alkalin ya bukaci a maida tsohon jami'in 'yansandan gidan yari kafin ya san hukuncin da zai yanke masa a mako mai zuwa. 

Kafin wannan hukuncin dai kungiyoyin kare hakkin bil'adama a kasar ta Kenya sun sha kokawa kan yadda 'yansanda a kasar suke azabtar da mutane ba tare da an hukuntansu ba. 

Denis Oketch kakakin hukumar "Sa ido a kan ayyukan 'yansanda mai zaman kanta" ya ce hukunci na yau wani hannunka mai sanda ne ga sauran jami'an 'yansandan kasar, don kowa daga cikinsu ya gudanar da ayyukansa bisa doka.