Kamaru : Amurka Ta Bukaci Tattaunawa Tsakanin Gwamnati Da 'Yan Ware
Gwamnatin Amurka ta bukaci gwamnati da masu fafatukar a ware na Kamaru dasu tattauna ba tare da wata-wata ba.
Da yake sanar da hakan a wani taron kwamitin MDD, kan sha'anin tsaro a yankin tsaikiyar Afrika, mukadashin jakadan Amurka a MDD, Jonathan Cohen, ya bukaci dukkan bangarorin dasu kawo karshen rikici, tare da tabbatar da zaman lafiya da kuma kawo karshen sabanin dake tsakaninsu ta hanyar tattaunawar siyasa.
A cewar jami'in, al'amuran tsaro dana ayyukan jin kai a yankin arewa maso gabashi da Kudu maso yamma na Kamaru sun fuskanci koma baya matuka, inda lamarin har ya kai ga haddasa cikas ga al'amuran jn kai.
Amurkar ta kuma bukaci shugaba Paul Biya, da ya gaggauta shirin cin gashin kan yankuna, sannan gwamnatinsa ta mutunta hakkin jin kai, tare da tabbatar da cewa MDD, da kungiyoyin agaji sun samu kaiwa ga jama'ar dake cikin bukata.
Tun a karshen shekara 2017 data gabata ne, masu fafatukar a ware a yankunan biyu na masu magana da turancin Ingilishi a Kamaru suka dauki makamai domin kawo karshen abunda suke kira nuna masu wariya da ake.