Albashi: Gwamnoni Zasu Sake Ganawa Da Shugaban Kasa Kan Albashin Ma'aikata.
Kungiyar gwamnoni a tarayyar Najeriya sun bukaci ganin shugaban kasa a karo na biyu dangane da mafi karancin albashi
Jaridar Premium times ta Najeriya ta ce shugaban kungiyar gwamnonin kuma gwamnan jihar Zamfara Abdulaziz Yari ya ki zantawa da yan jaridu bayan sun kammala taron nasu a jiya Alhamis da dare.
Amma shugaban bangaren yada labarai da hulda da jama'a na kungiyar Abdurrazaq Bello Barkindo ya sahidawa yan jaridu cewa, gwamnonin sun bukaci ganawa da shugaban kasa a yau Jumma'a kan batun mafi karancin Albashi, kuma wannan haduwar ita ce da karshe a wannan shekarar.
Barkindo ya ce a taron nasu na jiya gwamnonin sun yi maraba da gwamnan jihar Osun Adegboyega Oyetola wanda shi ne sabon gwamnan da ya shigi kungiyar sannan zama na jiya shi zama na farko da ya taba halata.
Kungiyar gwamnonin dai ta bukaci a sanya mafi karancin albashi a kan Naira dubu 22, a yayinsa gwamnatin tarayyar ta bukaci a sanya shi a kan Naira dubu 24 a yayinda kungiyar kwadago kuma ta bukaci a naira dubu 30.