Rikicin Kabilanci Ya Ci Rayukan Mutane Fiye Da 20 A Kasar Habasha
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i34443-rikicin_kabilanci_ya_ci_rayukan_mutane_fiye_da_20_a_kasar_habasha
Majiyar tsaron kasar Habasha ce ta sanar da cewa an yi rikicin ne a tsakanin al'ummun Oromos da Somali a yankin Moyele da ke kan iyaka da kasar Kenya
(last modified 2018-12-15T15:54:02+00:00 )
Dec 15, 2018 15:54 UTC
  • Rikicin Kabilanci Ya Ci Rayukan Mutane Fiye Da 20 A Kasar Habasha

Majiyar tsaron kasar Habasha ce ta sanar da cewa an yi rikicin ne a tsakanin al'ummun Oromos da Somali a yankin Moyele da ke kan iyaka da kasar Kenya

Kamfanin dillancin labarun Reuters ya ba da labarin cewa; Fadan da aka yi a ranakun alhamis da juma'a ya ci rayukan mutane 21 da kuma jikkata wasu 60

Mahukuntan kasar ta Habasha sun kuma sanar da cewa an sami kwararar mutane da dama daga yankin na Moyale domin su tsira da rayukansu daga rikicin. Wasu rahotannin sun ce an sami wadanda suka tsallaka iyaka zuwa cikin kasar Kenya da take makwabtaka da yankin

A cikin wannan shekarar ta 2018 an sami fadace-fadace a tsakanin al'ummar Oromos da saukin al'ummun da suke a yankin.

A farkon watan Aprilu na 2018 an tilasta wa wasu mutane fiye da dubu biyar yin hijira daa yankin bayan asarar rayukan da ta biyo bayan rkicin kabilanci